Tsohon dan kwallon kafa George Weah ya lashe zaben shugaban kasa a Laberiya

Tsohon dan kwallon kafar kasar Laberiya George Weah ya lashe zaben shugaban kasar inda zai maye gurbin shugaba Ellen Johnson-Sirleaf wadda ta yi shekaru 12 tana mulkin kasar.

A shekarun 2005 da 2015 Weah ya yi takarar shugaban kasa a Laberiya amma bai samu nasara ba.

Duk bayan shekaru 6 ne ake gudanar da zabe a Laberiya.

A shekarar 1995 Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta zabi Weah a matsayin dan wasan da ya fi kowanne a duniya.

Weah mai shekaru 51 ya buga wasanni 478 inda ya jefa kwallaye 193.Labarai masu alaka