Turkiyya na taka muhimmiyar rawa wajen kyautata rayuwar jama'ar Somaliya

Majalisar Dokokin Somaliya a ranar Talatar nan ta yaba wa gwamnatin Turkiyya bisa irin gudunmowar da ta ke bayar wa wajen jin dadin jama'ar kasar da kuma samar musu da kayan more rayuwa.

Mamba a majalisar dokokin da ke halartar wani taro a Afirka ta Kudu Lufti Sheriff Muhammad ya shaida wa manema labarai cewa, gwamnatin Turkiyya na taka muhimmiyar rawa a rayuwar 'yan kasar Simaliya.

Ya ce, ziyarar da shugaba Erdoğan ya kai a Somaliya a shekarar 2011 a lokacin da kasar ke cikin yunwa ta kara karfafa dangantakar kasashen 2.

Muhammad ya kara da cewa, a lokacin da Erdoğan ya je Somaliya ya ziyarci mutanen da aka raba da matsugunansu suke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira, maimakon ya fara zuwa fadar shugaban kasar. 

'Yan kasar Somaliya sun kalli wannan abu a matsayin so da kauna gare su.

Ya ci gaba da cewa, suna fata Turkiyya za ta kara yawan taimako da tallafin da ta ke ba wa kasar Somaliya.Labarai masu alaka