Cutar Kyandar Biri ta yadu wa a jihohi 7 na Najeriya

Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya ta bayyana cewa, an samu akallla mutane 31 da suka kamu da cutar Kyandar Biri a jihohin kasar 7.

Cutar Kyandar Biri ta yadu wa a jihohi 7 na Najeriya

Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya ta bayyana cewa, an samu akallla mutane 31 da suka kamu da cutar Kyandar Biri a jihohin kasar 7.

A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne Hukumar ta sanar da bullar cutar a jihar Beyelsa mai arzikin man fetur inda aka samu mutane 12 sun kamu da ita, kuma tuni aka killace mutane da dama.

Sanarwar da Hukumar ta fitar ta kara da cewa, jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da: Bayelsa, Rivers, Ekiti, Akwa Ibom, Legas, Ogun da Cross River. 

An bayyana cewa, an dauki samfurin jinin kowanne daga cikin wadanda cutar ta kama da ma na wadanda ake zargi da mu'amala da su inda ake jiran sakamako daga dakin bincike.

Hukumar ta yi kira ga mutane da su kasance masu kula da tsaftar jikinsu tare da nisantar wadanda suke dauke dawannan cuta.

Hukumar ta kuma ce, Birrai, Beraye da Kuregu ne ke harba wa dan adam wannan cuta.Labarai masu alaka