An kashe kusan mutane 100 a wani rikici a Sudan ta Kudu

Kusan mutane 100 ne suka mutu inda aka jikkata wasu da dama sakamakon sake barkewar sabon rikici tsakanin sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Lul Rai Koang ya bayyana cewa, an fafata rikicin a yankin arewa maso-gabashin kasar inda dukkan bangarorin 2 suke ikirarin samun nasara. 

Kakakin ya ce, a rikicin da aka yi a kusa da garin Waat na jihar Bieh an kashe sojoji 5 da 'yan tawaye 91.

Rahotanni sun ce rikicin ya afku a daidai lpkacin da ake kokarin sasanta bangarorin 2.

Koang ya kara da cewa, an fara rikicin tun ranar Lahadi bayan 'yan tawayen sun kai musu hari inda aka ci gaba da arangama har zuwa ranar talatar da ta gabata. 

Amma mai magana da yawun 'yan tawayen Mabior Garang ya zargi sojojin gwamnatin da karya yarjejeniyar tsagaita wuta inda ya ce, sun kashe sojoji da dama a rikicin.Labarai masu alaka