Sanagal ta rufe makarantun 'yan ta'addar FETO

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar da ke Yammacin Afirka ta bayyana cewa, an rufe makarantu 15 da suke da suna Yavuz Selim inda aka sanya jami'an 'yan sanda suna kula da su.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Sanagal Aly Ngouille Ndiaye ya shaida wa jaridar Daily Walfijir cewa, yana bukatar dukkan iyayen yara da su bar yaransu a gida. Saboda makarantun za su kasance a rufe.

Wannan umarni ya biyo bayan bukatar hakan da gwamnatin Turkiyya ta mika wa Sanagal na ta rufe makarantun FETO da suka yi yunkurin kifar da zababbiyar gwamnati a ranar 15 ga watan Yulin 2016.

Turkiyya dai ta zargi shugaban FETO da ke Amurka Fethullah Gulen da yin makarkashiya a tsawon lokaci wajen ganin an kifar da gwamnatin kasar.

Gwamnatin Turkiyya ta kafa Asusun Ma'arif wanda ya ke karbe makarantun 'yan ta'addar tare da ci gaba da kula da su.Labarai masu alaka