An yanke hukuncin kisa ga sojan da ya harbe Minista a Somaliya

Kotun sojoji a Somaliya ta yanke hukuncin kisa ga wani soja da ya harbe Ministan da ya fi kowanne karancin shekaru a Somaliya Abbas Suraj.

Shugaban kotun sojin Somaliya Hassan Ali Nur Shute ya sanar da cewa, shaidar da aka samu na nuna yadda sojan Ahmad Abdullah Abdi ya bindige ministan aiyuka na kasar Suraj a ranar 3 ga watan Mayu.

Hassan ya ce, sojan ya harba harsashai sau 3 a kan motar da ministan ke ciki kuma daya ya same shi a ka wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Ya ce, an samu bidiyo da hotunan da ke nuna yadda aka yi kisan a kusa da fadar shugaban kasar da ke birnin Mogadishu.

Bayan rayuwa a matsayin dan gudun hijira, Suraj ya zama dan majalisar dokokin Somaliya mafi karancin shekaru a watan Nuwamban bara kuma ya zama minista a watan Fabrairu.

Sojan da yi kisan gillar ya kasance yana tsaron lafiyar odita Janar na Somaliya Nur Farah

AALabarai masu alaka