An kawo karshen kawanyar da Al-Shabab ta yi wa Mogadishu

Jami’an tsaro sun kawo karshen kawanya ta wanni 10 da ‘yan ta’addar Al-Shabab suka yi wa Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

An kawo karshen kawanyar da Al-Shabab ta yi wa Mogadishu

Jami’an tsaro sun kawo karshen kawanya ta wanni 10 da ‘yan ta’addar Al-Shabab suka yi wa Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

Wani jam’in dan sanda Ali Adnan ya shaida wa ‘yan jaridu cewa, ‘yan ta’addar Al-Shabab sun kai dauki kan wani gidan sayar da Pizza bayan kai harin kunar bakin wake a otel din Posh da ke kusa da gurin.

Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida ta Somaliya Ahmad Muhammad ya ce, jami’ansu sun kawokarshen kawanyar da Al-shabab ta yi wa birnin Mogadishu na tsawon awanni 10.

Ya kara da cewa, akalla akwai mata 7 da wani dan kasar Siriya 1 da suka jikkata.

Ya kuma ce, an kubutar da ‘yan kasar Kenya 2 da dan kasar Itopiya daya daga hannun ‘yan ta’addar.

Kungiyar ta’adda ta Al-Shabab kuma reshen Alqa’eda da ke Somaliya ta dauki alhakin kai hare-haren.Labarai masu alaka